in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen raya tattalin arzikin duniya
2015-09-12 13:11:49 cri
A jiya Jumma'a 11 ga wata, aka rufe dandalin tattaunawar tattalin arziki na Davos na yanayin zafi a birnin Dalian na Sin. A yayin dandalin kuma, masana da yawa daga Sin da ketare sun hallara a gu daya domin yin shawarwari kan "Tsara sabuwar taswirar samun ci gaba" har sama da sau 10. A matsayin kasar da ta shirya wannan dandalin tattaunawa, an fi mai da hankali kan yanayin da kuma makomar raya tattalin arziki ta kasar Sin.

Mahalarta dandalin da dama sun bada kwarin gwiwa sosai kan bunkasuwar tattalin arzikin Sin. A ganin su, kamata ya yi a gaskata makomar bunkasuwar tattalin arzikinta. Ko da yake za a gamu da tangal tangal a yayin kyautata tsarin, amma Sin tana ba da gudummawa sosai wajen tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki a halin yanzu da ake ciki na fuskantar babbar matsalar hada hadar kudi a kasashen duniya.

Farfesa Lin Yifu dake aiki a kwalejin nazari kan bunkasuwar kasa da kasa na Jami'ar Peking ya bayyana cewa, ya yi imani sosai da cewa, yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kimanin kashi 7 cikin dari, kuma ba shakka Sin za ta cimma wannan buri.

Farfesa Lin ya kara da cewa, ba kamar yadda wasu kasashe masu sukuni da kasashe masu tasowa suke ba, yawan albashin gwamnatin kasar Sin ya kai kashi 40 cikin dari na GDP kawai, kuma gwamnatin kasar ta samu damar ajiyar kudin Amurka sama da biliyan 3000, jama'ar kasar su ma sun saba da ajiye kudi a bankuna. A sabili da haka, Sin tana da karfin tabbatar da karuwar yawan jarin da za ta zuba, ta yadda jama'ar kasar za su kara samun kudin shiga da kara kashe kudi.

Bayan haka, farfesa Lin ya ce, yanayin da ake ciki a nan kasar Sin ba zai sami babbar sauyawa ba, dan haka zai tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar lami lafiya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China