in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya yi shawarwari tare da wakilan 'yan kasuwa masu halartar dandalin tattaunawa na Davos
2016-06-29 11:35:34 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi shawarwari tare da wakilan 'yan kasuwa masu halartar dandalin tattaunawa na Davos fiye da 300 a cibiyar taruka ta Meijiang dake birnin Tianjin na kasar Sin a ranar 28 ga wata da safe.

Li Keqiang ya bayyana cewa, yanzu ana kokarin yin kwaskwarima kan tsari, musamman a fannin samar da kayayyaki, da sa kaimi ga yin kwaskwarima kan rage biyan haraji, da gudanar da manufofin samun bunkasuwa ta hanyar yin kirkire-kirkire, da bunkasuwar sabon tsarin tattalin arziki har ya zarce hasashen da aka yi, wanda ya samar da gudummawa ga samar da aikin yi ga jama'a, da kuma samun ci gaba a fannin kyautata tsarin samar da kayyayaki.

Li Keqiang ya kara da cewa, yanzu ana kokarin sa kaimi ga kyautata tsarin tattalin arzikin Sin a karkashin yanayin bude kofa ga kasashen waje, da kara samar da sharadin shiga kasuwanci, da samar da yanayin yin takara cikin adalci, da kuma kafa kasuwar zuba jari, da jawo jari mai kyakkyawar makoma a duniya.

A nasa bangare, shugaban dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya Klaus Schwab ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu muhimmin matsayi a duniya a fannin tattalin arziki. Li Keqiang ya bayyana burin bunkasuwar kasar Sin a gun dandalin tattaunawar a wannan karo, kana ya yi bayani game da matakan sa kaimi ga yin kwaskwarima da bude kofa, wadanda za su sa kasa da kasa su kara yin imani ga bunkasuwar kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China