in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
PLO ta yi kira ga kasashen duniya da su hana Isra'ila ta gina matsugunan Yahudawa
2016-08-15 10:19:03 cri

Babban sakataren hukumar gudanarwar kungiyar kwatar 'yancin Palesdinu ta PLO Mista Saeb Erekat ya yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa Isra'ila lamba domin hana ta ci gaba da gina matsugunan Yahudawa.

Wata sanarwa da Saeb Erekat ya bayar a jiya Lahadi 14 ga wata ta bayyana cewa, gina matsugunan ya sabawa dokakin kasa da kasa, kuma Isra'ila ta dauki wannan mataki ne da nufin kwace filaye da dukiyoyin Palesdinu, wanda kuma ya kawo illa ga manufar kafa kasashen biyu. Sanarwar ta kuma nuna cewa, tuni Saeb Erekat ya aike da wasiku ga ministocin harkokin wajen kasashe da dama don neman kasashen duniya da su dauki mataki nan take da ya dace na hana Isra'ila gina matsugunan Yahudawa.

Ban da wannan kuma, Saeb Erekat ya bayyana a cikin sanarwar cewa, a watan Yulin bana, Isra'ila ta hanzarta gina irin wadannan matsugunai. A saboda haka ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakai na dakatar da wannan aiki, sannan ya bukaci kungiyoyi da kamfannoni na kasa da kasa da su kauracewa kayayyakin da aka samar daga wadannan matsugunai.

Dadin dadawa, sanarwar ta ruwaito wani rahoton da kungiyoyin masu ra'ayin rikau mai suna 'Peace Now' ta Isra'ila ta fitar, wanda ke cewa, gwamnatin Isra'ila ta amince da wadansu shirye-shirye da dama a cikin shekaru 4 da suka gabata da zummar halata matsugunai 14, tare da gina wasu sabbi 20. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China