in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin kasashen BRICS sun nanata aniyar hadin kai wajen samar da abinci
2017-06-18 12:04:20 cri
Ministocin mambobin kasashen BRICS sun jaddada muhimmancin yin hadin gwiwa domin tunkarar batun samar da abinci a lokacin da suka karkare taronsu a ranar Asabar.

Cikin wata yarjejeniyar da mambonin kasasshen suka rattaba hannu a lokacin taron wuni uku na ministocin, sun ambaci muhimmancin tunkarar batutuwa da suka shafi inganta yanayin zamantakewar al'umma, tattalin arziki da kuma kiyaye muhalli domin samar da dauwwamaman ci gaba wajen inganta fannin samar da abinci.

Yarjejeniyar ta nuna cewa, ministocin sun amince da yin hadin gwiwa tare, domin gudanar da muhimman batutuwan ci gaba da kawar da shinge game da sha'anin mu'amalar cinikayya da tattalin arziki.

Kana sun amince za su bullo da sabon tsari na warware matsalar da ta shafi sauyin yanayi.

Yarjejeniyar ta kuma nuna cewa, BRICS ta himmantu matuka wajen yin amfani da fasahar kirkire kirkire domin magance matsalar abinci, da bunksa aikin gona da kuma inganta muhalli.

Ministocin sun cimma matsaya cewa, muddin ana son bunkasa aikin gona na zamani, ya zama tilas a rungumi hanyoyin amfani da sabbin fasahohin zamani da tabbatar da sabunta hadin kai don cimma wannan buri. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China