in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya taya kasashen BRICS murnar shirya gasar wasanni
2017-06-18 11:58:53 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar gasar wasanni na kasashen BRICS na 2017 wanda aka bude a ranar Asabar a birnin Guangzhou na ksar Sin.

Shirya gasar wasannin a karon farko wani muhimmin ci gaba ne ga kasashen na BRICS, tun bayan da aka cimma matsayar shirya shi a lokacin taron koli na mambobin kasashen na BRICS a Goa a shekarar 2016.

Kowace mamba a cikin kasashen na BRICS ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da shirya gasar, shugaba Xi ya ce, ya yi amana cewa gasar wasannin ta BRICS za ta samar da damammaki gare su, da bunkasa wasannin gargajiya, da kuma inganci ci gaban fannin wasanni wajen kara samun fahimtar juna da abokantaka tsakanin al'ummomin kasasashen.

Xi ya ce yana fatan dukkan bangarorin mahalarta wasannin za su nuna jajurcewa domin ciyar da fanninn wasanni gaba.

Wasannin ya kunshi dukkan kasashen mambobin na BRICS, da suka hada da Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afrika ta kudu, wanda ya shafi zagaye 10 na nau'i kan wasanni uku da ya hada da wasan kwallon Kwando na maza, da volleyball na mata da kuma wasan takobi. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China