in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tana makokin mutuwar jami'anta a Mali
2017-05-24 09:29:24 cri
A jiya Talata MDD ta gudanar da zaman makoki sakamakon rayuwar wasu daga cikin jami'an MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a Mali, kakakin MDDr ne ya tabbatar da hakan.

Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD, ya ce, jami'an biyu na tawagar aikin wanzar da zaman lafiya ta MDD a Mali wato MINUSMA sun gamu da ajalinsu ne, a lokacin wani kwantan bauna da aka yi musu a wani waje mai nisan kilomita 5 daga Aguelhok, a yankin Kidal.

Kakakin ya ce, wani guda daga cikin jami'an wanzar da zaman lafiyar ya samu raunuka.

Shugaban tawagar ta MINUSMA, Mahamat Saleh Annadif, ya jaddada cewa wadannan munanan hare-haren da ake kaddamarwa kan fararen hula, da jami'an wanzar da zaman lafiyar na kasa da kasa, da dakarun gwamnatin Mali a 'yan makonnin da suka gabata manufar hare haren shi ne yunkurin dakile kokarin da dakarun ke yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Mali.

Babban sakataren MDD ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda hare haren ya rutsa da su, Dujarric, ya kara da cewa MDD za ta yi tattaunawa mai zurfi game da batun jami'an na MINUSMA a lokacin zamanta. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China