in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da harin da aka kai ga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya a Mali
2017-05-24 15:15:14 cri
Jiya Talata, kwamitin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa, inda ya yi Allah wadai da kakkausan harshe kan harin da aka kai ga ma'akatan kiyaye zaman lafiya da MDD ta tura zuwa kasar Mali, sannan ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta gurfanar da masu aikata wannan laifi gaban kuliya cikin sauri.

Sa'an nan, kwamitin sulhu na MDD ya nuna damuwarsa matuka kan yanayin tsaron kasar Mali, inda ya sa kaimi ga bangarorin kasar da abin ya shafa da su aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ba tare da bata lokaci ba, domin kyautata yanayin tsaron kasar, ta yadda za a cimma burin shimfida zaman lafiya da zaman karko a kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China