in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala aikin jefa kuri'ar zaben shugabancin Iran
2017-05-20 14:03:35 cri
An kammala jefa kuri'a a babban zabe karo na 12 a kasar Iran.

Da misalin karfe 8 na safiyar jiya Jumma'a ne, babban jagoran addini na kasar Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya jefa kuri'a ta farko a wata mazaba da aka kafa a fadarsa dake birnin Tehran, daga nan ne kuma aka soma kada kuri'ar zaben shugaban kasar.

An yi hasashen cewa, adadin mutanen da suka jefa kuri'ar ya zarce kashi 70 bisa dari.

Jimilar Iraniyawa 1,636 ne suka yi rajistar shiga babban zaben a wannan karo, ciki har da shugaban kasa na yanzu Hassan Rouhani da sauran wasu 'yan takara guda biyar, wadanda suka samu tantancewa daga kwamitin sa ido kan harkokin zabe na kasar.

Amma daga bisani 'yan takara biyu sun janye, don haka a karshe mutane hudu ne suka tsaya takarar.

A wata sabuwa kuma, da misalin karfe 9 na safiyar yau Asabar agogon kasar Iran ne, hedkwatar kula da harkokin zaben kasar ta sanar da cewa, sakamakon farko na babban zaben kasar ya bayyana cewa, shugaban kasa mai ci, kana dan takara mai rajin kawo sauye-sauye Hassan Rouhani na kan gaba. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China