Wannan mataki dai wani bangare ne na yarjejeniyar da kasashen 5 tare da Iran din suka amincewa, karkashin shirin JCPOA, yayin shawarwari game da shirin Iran din na sarrafa makamashin nukiliya da ya gudana a birnin Vienna cikin watan Yulin shekarar 2015.
Karkashin yarjejeniyar ta Vienna, Iran ta amince da ta sake fasalin wannan cibiyarta, ta yadda za ta rage yawan sinadarin plutonium da za a iya samarwa a cibiyar, tare da kaucewa sarrafa makamai masu alaka da sinadarin.
A kuma taron na Vienna ne kasashe 5 da suka kunshi Sin, da Amurka, da Rasha, da Faransa, da Jamus, da Birtaniya, tare da ita kanta Iran suka amince Sin da Amurka, su yi aiki tare wajen ganin an sauya fasalin waccan cibiya ta Arak. (Saminu Hassan)