in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka mutu a tagwayen harin ta'addanci a Iran ya karu zuwa 13
2017-06-08 10:16:52 cri
A kalla mutane 13 ne aka hakikance sun mutu a sanadiyyar tagwayen hare haren ta'addanci da wasu mahara suka kaddamar a majalisar dokokin Iran da kabarin Imam Khomeini babban birnin kasar Tehran a ranar Laraba.

Mataimakin ministan harkokin cikin gidan kasar Iran mai kula da harkar tsaro ,Hossein Zolfeghari, shi ne ya tabbatar da hakan a wani jawabi ta gidan talabijin na IRIB TV na kasar. Kana mutane 43 ne suka samu raunuka a sanadiyyar hari ta'addancin in ji jami'in.

Bugu da kari, dukkan maharan hudu da suka kaddamar da hare haren a majalisar dokokin kasar da kabarin na Khomeini sun mutu.

Rahotanni na cewa, tuni kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Islama ta IS ta dauki alhakin kai hare-haren.

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da kakkausar murya game da harin ta'addancin da aka kaddamar a kabarin Ayatollah Ruhollah Khomeini, da ginin majalisar dokokin wato (Majlis) a birnin Tehran, na kasar Iran.

Guterres, ya bukaci daukar matakan shari'a kan wadanda suke da hannu wajen kitsa irin wadannan hare hare na ta'addanci. Kana ya bayyana cewa yaki da ta'addanci hakki ne da ya rataya a wuyan dukkan kasashen duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China