in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rouhani ya lashe zaben shugabancin kasar Iran da kashi 57 cikin 100
2017-05-21 13:24:26 cri

Shugaban kasar Iran mai ci Hassan Rouhani shi ne wanda ya lashe zaben shugabancin kasar, ministan ma'aikatar harkokin cikin gidan Iran, Abdolreza Rahmani Fazli, shi ne ya sanar da hakan jiya Asabar.

Rahmani Fazli ya ce, daga cikin kuri'u miliyan 41, da dubu 220, da 131 da aka kada a zaben kasar a Juma'ar da ta gabata, Rouhani ya samu kuri'u miliyan 23, da dubu 549, da 616 wato kashi 57 bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada.

Dan takarar dake bi masa baya shi ne Ebrahim Raisi, wanda ya samu kuri'u miliyan 15, da dubu 786,da 449 wato kashi 38.5 bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada.

A bisa dokar kasar, dukkan 'yan takarar dake da wani korafi game da sakamakon zaben, za su iya gabatar da korafin nan da kwanaki uku ga majalisar dokokin kasar Iran, in ji Fazli.

Majalisar ce ke da karfin fada aji game da sha'anin dokoki a kasar, kuma ita ce za ta tabbatar da sahihancin sakamakon zaben shugaban kasar.

Kimanin Iraniyawa miliyan 56 ne suka cancanci kada kuri'a a kasar, kuma sama da akwatunan zabe 60,000 ne aka rarraba a duk fadin kasar domin jefa kuri'un a zaben kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China