Mai horas da kungiyar kwallon kafa na Super Eagles ta Najeriya Gernot Rohr ya bayyana cewa, wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka da kungiyar za ta yi da 'yan wasan Bafana Bafana na kasar Afirka ta kudu zai kasance mai matukar wahala.
Rohr wanda ya bayyanawa manema labarai hakan bayan kammala atisayen su na farko a filin wasa na Godswill Akpabio na kasa da kasa dake Uyo, ya ce, ba a taba doke 'yan wasan Bafana Bafana a dukkan wasannin da suka yi cikin shekarun biyun da suka gabata ba, kana mai tsaron raga da kyaftin din kungiyar dukkansu ba za su buga wasan ba don haka wannan babban kalubale ga kungiyar ta Super Eagles.
Sai dai ya shaidawa manema labarai cewa, akwai wasu karin 'yan wasa guda hudu da yake sa ran za su iso sansanin samun horon kungiyar. Kuma 'yan wasan suna cikin koshin lafiya.
'Yan wasan na Super Eagles dai za su kara ne da kasar Afirka ta kudu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafan Afirka na shekara 2019 a filin wasa na Godwin Akpabio dake Uyo.(Ibrahim)