Sanarwar da kakakin rundunar Sojin Pakistan ya fitar, ta ce tawagar dakarun ta Nijeriya, wadda ta kunshi jami'ai 440 ciki har da hafsoshi 26, ta kammala karbar horon ne a jiya Alhamis.
Babban hafsan sojin Pakistan Janar Qamar Bajwa ya kai ziyara a jiyan, ga dakarun na musammam da suka samu horo a kusa da garin Terbela na arewa maso yammacin lardin Khyber Pakhtunkwa, domin ganewa idonsa matakin karshe na horon da dakarun musammam na kasar suka ba takwarorinsu na Nijeriya.
Janar Bajwa, ya yaba da irin ingancin horon da aka bayar da kuma sakamakon da aka samu daga wadanda aka horar.
Ya ce rundunar sojin Pakistan ta na da kwarewa a fannoni daban-daban ta fuskar yaki da ta'addanci tare kuma da kayakin aiki na zamani, inda ya ce suna murnar taka rawa wajen inganta yaki da ta'addanci a kasashe kawayen Pakistan da dama.
Mukaddashin jakadan Nijeriya a kasar Salisu Murtala Isa da manyan hafsoshin sojin Nijeriya, na daga cikin wadanda suka halarci bikin yaye dakarun. (Fa'iza Mustapha)