in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotu a Nijeriya ta kori shari'ar da ake wa shugaban majalisar dattijan kasar
2017-06-15 09:49:14 cri
Kotun da'ar ma'aikata ta Nijeriya wato CCT, ta kori shari'ar da ake wa shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, tare da wanke shi daga zargin da ake masa na kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

Gwamnatin Nijeriya ce ta gurfanar da Bukola Saraki bisa zarginsa da laifuka 18 da ke da jibi da kin bayyana kadarorinsa.

Kotun da'ar ma'aikata karkashin mai shari'a Danladi Umar ce ta kori karar bisa la'akari da cewa, bangaren shigar da kara ya gaza bada kwararan hujjoji.

Kotun ta ce shaidun da aka gabatar ba su isa ba, sannan kuma ba su da karfi.

Har ila yau, kotun ta kuma daukaka cewa, babu wata shari'a game da Saraki, tana mai jadadda cewa a lokacin da ake tantance shaidun da bangaren shigar da kara ya gabatar an gano ba su da sahihanci, dan haka ba za a iya dogaro da su ba.

Har ila yau, kotun ta CCT ta ce babu wata kotu da ta san aikinta da za ta yankewa Saraki hukunci bisa hujjojin da bangaren shigar da kara ya bayar ta hannun shaidunsa 4.

A ranar 23 ga watan Fabreru ne gwamnati ta sake gurfanar da Saraki a gaban kotu bisa zarginsa da laifuka 18 da aka yi wa gyara, game da kin bayyana ainihin kadarorin da ya mallaka, bayan ayarin lauyoyi masu shigar da kara karkashin Rotimi Jacobs ya shigar da karar da aka gyara a ranar 8 ga watan Fabrerun.

Tun farko, Shugaban Majalisar Dattijan Bukola Saraki na fuskantar shari'a ne bisa tuhume-tuhume 18 da suka danganci kin bayyana kadarorin da ya mallaka tun lokacin da yake gwamnan jihar Kwara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China