An bude taron na ranar Laraba ne da taken "sauya alkiblar sufuri da inganta tsarin gudanarwa da zirga-zirgar al'umma", kuma masu ruwa da tsaki na ganin za a iya amfani da tsarin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da sassa masu zaman kansu don cimma wannan buri.
Da yake jawabi yayin taron, babban sakatare a ma'aikatar sufurin kasar Sabi'u Zakari, ya ce za a yi amfani da sabbin dabarun kirkire-kirkire wajen cimma nasarar burin da aka sanya gaba a matakai na jihohi da na tarayyar kasar.
Mr. Zakari ya kara da cewa, surufi muhimmin mataki ne ga bunkasar tattalin arzikin Najeriya, tare da inganta harkokin bada hidima. A cewarsa, sufuri ta titunan mota na daukar kaso 90 bisa dari, na hidimomin sufuri a Najeriya, don haka ya dace a baiwa sashen kulawar da ta dace. (Saminu Hassan)