Kwamishinan 'yan sandan jihar Agyole Abeh, ya shaidawa wani taron manema labarai a Kaduna cewa, rahoton karya ne tsagwaronsa, da ke neman jefa tsoro a zukatan al'umma.
Agyole Abeh ya ce rahoto da rundunar ta samu a baya-bayan nan shi ne wanda aka tare wasu mutane 5 akan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda aka yi wa 3 daga cikinsu fashi tare kuma da sace wasu guda biyu.
Kwamishinan ya ce babu yadda za a yi a sace mutane 20 dake tafiya tare a mota guda, ba tare da sanin inda aka yi da su ko kuma samun rahoto daga iyalansu ko shaidun gani da ido ba. (Fa'iza Mustapha)