in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata bullo da sabbin dabarun yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi
2017-05-12 12:42:21 cri
Hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi ta Najeriya zata fara amfani da sabbin dabarun dakile ta'ammali da haramtattun kwayoyi.

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasar (NDLEA), Muhammad Abdallah, shi ne ya bayyana hakan a lokacin wani taro da manyan kwamandojin hukumar a garin Jos dake shiyyar arewacin kasar.

Taron dandalin mai taken, "Bunkasa NDLEA domin amfani da ingantattun dabaru wajen aiwatar da dokokin da suka shafi yaki da haramtattun kwayoyi" ana saran taron zai nazarci wasu batutuwa da suke kawo nakasu game da ayyukan hukumar

Abdallah ya jadddawa kwamandojin muhimmancin zage damtse game da ayyukan hukumar, yana mai cewa bai kamata jami'an su yi kasa a gwiwa ba.

Kasar ta yammacin Afrika ta zama tamkar zango ne na jigilar haramtattun kwayoyi da hodar cocaine zuwa kasashen Turai, da Amurka.

Hukumar NDLEA ta sha kama haramtattun kwayoyi a filin jirgin sama na Murtala Mohammed (MMIA) dake birnin Legas wadanda aka shigo dasu kasar. Hakan ya sa masu safarar muggan kwayoyin suke amfani da hanyoyi ta ruwa da kan tudu domin kudun kada a damke su a filin jirgin saman na MMIA.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China