in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijer ta tsawaita dokar ta baci don fuskantar kalubalen ta'addanci
2017-06-18 12:54:50 cri
Shugaban kasar Nijer Mahamadou Issoufou ya bayyana a ran 16 ga wata cewa, gwamnatin kasar ta tsai da kudurin tsawaita dokar ta baci ta tsawon watanni uku a lardin Diffa dake kudancin kasar da wasu larduna guda shida dake yammacin kasar, domin fuskantar kalubaloli na ta'addanci.

Bugu da kari, ya ce, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Boko Haram tana kalubalantar yanayin tsaron lardin Diffa kwarai da gaske, haka kuma, wasu kungiyoyin ta'addanci dake kasashe makwabta, kamar su Libya da Mali, sun kawo barazana ga yanayin tsaro a galibin yankunan dake yammacin jamhuriyar Nijer, watau yankin Sahel. Shi ya sa, aka tsai da kudurin tsawaita dokar ta bacin a wadannan yankuna. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China