in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministar harkokin wajen Ghana ta jadadda rawar da matasa za su taka wajen samar da ci gaban Afrika
2017-05-26 09:25:44 cri
Ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, ta jadadda muhimmancin rawar da matasa za su taka wajen tabbatar da hadin kai da ci gaban nahiyar Afrika.

Shirley Botchwey da ta bayyana haka a jiya Alhamis, ta kuma yi kira ga shugabannin da masu ruwa da tsaki su mai da hankali wajen ba matasa damar bada gudunmuwarsu ga tabbatar da ci gaba da zaman lafiya da hadin kai.

Ta ce muradin samar da hadin kai a Afrika da shugabbnin a nahiyar ke fafutukar tabbatarwa, na da matukar muhimmanci ga ci gaban nahiyar, saboda muradin zamewar nahiyar tsintsiya madaurinki daya, shi ne ke karfafa dangantaka tsakanin kasashe mambobin tarayyar Afrika.

Ministar na wannan jawabi ne yayin kaddamar da bikin baje kolin hotuna da aka yi a Accra, babban birnin Ghana, a wani bangare na bikin ranar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China