Rahotanni na nuna cewa, a kalla kamfanonin kasar Sin 50 daga bangarorin masana'antu daban-daban ne suka baje kolin kayayyakinsu, a wani mataki na samar da kafar yin hadin gwiwa da 'yan kasuwan kasar Ghana.
Kasashen Sin da Ghana sun amfana da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu, tun lokacin da kasashen biyu suka kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu shekaru 57 da suka gabata.
A shekarar da ta gabata yawan kudin cinikayya tsakanin kasashen biyu ta kai dala biliyan 5.976