in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira da a ba kasashen Afirka damar warware matsalolinsu da kansu
2017-06-16 14:57:28 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa, kungiyar tarayyar Afirka wato AU da sauran hukumomin nahiyar Afirka suna nuna fifiko kuma suna da kyawawan dabarun warware batutuwan da ke daukar hankali a nahiyar ta Afirka.

Liu Jieyi ya yi wannan kira ne a ranar 15 ga wata, inda ya ce kamata ya yi kwamitin sulhu na MDD ya girmama tunanin da shirye-shirye da kasashen Afirka suka gabatar, sannan ya girmama ikon mulkin kasashe masu ruwa da tsaki da kuma ra'ayoyinsu, tare da inganta tuntubar wadannan hukumomi, a kokarin hada kansu wajen daidaita batutuwa a siyasance.

A wannan rana, kwamitin sulhu ya shirya budadden taro don nazarin batun yin hadin gwiwa tsakanin MDD da AU.

Har ila yau, Liu Jieyi ya ce kasar Sin ta yi alkawarin bai wa AU tallafin kudi ta fuskar aikin soja a kyauta kafin shekarar 2020, wanda jimillarsa ta kai dalar Amurka miliyan dari 1.

Bugu da kari, asusun wanzar da zaman lafiya da ci gaba na Sin da MDD ya fara aiki a hukumance, wanda zai taimaka wa MDD wajen gudanar da shirin shimfida zaman lafiya da ci gaba a nahiyar ta Afirka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China