in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara saukaka hanyoyin zuba jari
2017-03-24 15:39:58 cri
Mataimakin firayiministan kasar Sin Zhang Gaoli ya ce kasar Sin za ta zurfafa tare da saukaka hanyoyin zuba jari ga masu sha'awar zuba jari na kasashen ketare.

Zhang Gaoli, ya ce kasar za ta samar da kyakkyawan yanayin ga masu zuba jari, yana mai cewa, damarmaki iri guda masu zuba jari na cikin gida da na kasashen waje za su samu.

Ya kara da cewa, kasar Sin za ta fadada tare da bunkasa shirin ciniki cikin 'yanci, tare da zama na daya wajen samu masu zuba jari daga kasashen waje.

Mataimakin Firayiministan ya ce ana karfafawa masu zuba jarin gwiwar shiga a dama da su cikin manyan manufofin yakin da kuma zuba jari a fannonin kare muhalli, sarrafa kayyaki da fannonin da suka zama koma baya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China