Rahoton ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2005, yawan jarin da Sin ta zuba a kasashen waje kai tsaye yana karuwa a shekaru 10 a jere, yawansa a shekarar 2015 ya kai dala biliyan 145.67.
Rahoton ya yi bincike game da makomar tattalin arzikin kasashen da aka zuba jari bisa shirin "Ziri daya da hanya daya", kashi 73 cikin dari na kamfanonin da aka yi bincike sun nuna kyakkyawar fata, a cikinsu kashi 44 cikin dari suna shirin fadada zuba jari. (Zainab)