in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan jarin da Sin ta zuba a ketare a shekarar 2016 ya kai sabon matsayi
2017-01-13 11:00:15 cri
Cibiyar AEI ta kasar Amurka, wata shahararriyar cibiya ce ta ba da shawarar kwararrun kasar, ta fidda wani sabon rahoto kan mujallar "China Global Investment Tracker", inda ta bayyana cewa, jarin da kasar Sin ta zuba a ketare a shekarar 2016 ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 175, wato dai adadin ya karu da kashi 50 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, haka kuma kasar ta karya matsayin tarihinta a fannin zuba jarin waje.

Sanannen marubucin mujallar, kuma masani a cibiyar nazarin masana'antun kasar Amurka shehun malami Derek Scissors, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da zuba jari a ketare a shekarar 2017, kana masana'antun kasar za su karfafa ayyukansu na zuba jari da hadewa, sai dai mai yiwuwa ne yawan masana'antun da za su yi ayyukan, da wadanda suka cimma nasara a fannin za su ragu. (Bilkisu Xin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China