Mataimakiyar wakiliyar asusun a Najeriya Eugene Kongnyuy ce ta bayyana hakan a Abuja lokacin da take mika wasu kayayyakin kula da lafiya ga 'yan matan na Chibok 106 da aka ceto wadanda a halin yanzu ke cibiyar gyaran tunani.
Ta ce asusun ya samar da wadannan hidimomi ga yaran ne tare da taimakon wasu abokan hulda gami da kokarin gwamnatin tarayya da na jihohin kasar.
Kayayyakin da asusun ya baiwa 'yan matan na Chibok sun hada da kayayyakin sakawa na gargajiya da 'yan kwalaye, kananan wanduna ko kamfai, audugun mata, sabulu, man goge baki da tawul din wanka. Haka kuma asusun ya himmantu wajen ganin an dawo da martaba da kimar 'yan matan da aka ceto.
A nata jawabin yayin bikin ministar mata da walwalar jama'a ta Najeriya, Aisha Alhassan ta bayyana cewa, gwamnati ta yi na'am da irin taimakon da asusun ke bayarwa, musamman wajen farfado da kayayyakin dake cibiyar da aka tsugunar da 'yan matan da biyan kudaden albashin ma'aikatan da ke kula da su da kayayyakin amfanin yau da kullum da kuma dabarun gyara tunani. (Ibrahim Yaya)