Suleiman Adamu wanda ya bayyana haka a jiya Talata, ya ce za a aiwatar da aikin ne da hadin gwiwar gwamnatin Hungary domin lalubo yadda za a samar da kariya da zai kare bakin koguna da yankunan koguna da ke fuskantar ambaliyar ruwa.
Ministan ya ce duk da muhimmin aikin zai dauki lokaci, ma'aikatar ta fara tattaunawa da masana daga kasar Hungary.
Kogin mai nisan kilomita 4,280 da fadin murabba'in kilomita miliyan 2.2, ya samo asali ne daga yankin Faranah na kudu maso gabashin Conakry, inda ya ratsa ta kasashen Afrika da suka hada da Guinea da Mali da Niger da Benin da kuma Nijeria, ya kuma dangana zuwa tekun Atlantika.
Suleiman Adamu ya ce ma'aikatarsa za ta samar da kudin aiwatar da aikin ne da hadin gwiwar bangarori masu zaman kansu, yana mai jadadda cewa, ya kamata a ce Nijeriya tana da yankuna noman rani ba tare da fuskantar barazanar ambaliya ba. (Fa'iza Mustapha)