in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta yi gargadi game da barkewar cutar murar tsuntsaye
2017-06-03 12:07:40 cri
Gwamnatin Nijeriya ta gargadi al'umma, game da barkewar cutar murar tsuntsaye a babban birnin tarayyar kasar Abuja, da kuma wasu jihohi bakwai.

Daraktan sashen kula da dabbobi da yaki da kwari Gideon Mshelbwala ne ya yi gargadin a jiya Juma'a, lokacin da yake ganawa da kwamishinonin harkokin noma na jihohi a Abuja.

Gideon Mshelbwala, ya ce jihohin da aka samu barkewar cutar sun hada da Bauchi da Kano da Katsina da Nasarawa da Filato da babban birnin kasar da kuma Kaduna da aka samu rahoton bullar cutar a ranar 30 ga watan Mayu.

Ya ce tun da cutar ta barke a kasar cikin shekarar 2008, ta yadu zuwa jihohi 26 da kuma babban birnin kasar, sannan ta shafi gonaki 800 a yankunan kananan hukumomi da ba za su gaza 123 ba.

Daraktan wanda ya ce har yanzu babu rigakafin cutar a kimiyyance. Ya ce gwamnati na daukar matakan dakile yaduwar cutar da suka hada da kebe tsuntsaye da kawar da su zuwa wani wuri da kashe wadanda suka kamu da kuma matakan kariya na takaita yaduwar cututtuka a gonaki.

Gideon Mshelbwala ya kuma bayyana rashin jin dadi game da yadda manoma ba sa daukar matakan kariya da muhimmanci, yana mai cewa shi ne babban dalilin dake sa cutar kara yaduwa.

Ya gargadi manoma a kan yi wa tsuntsayen rigakafi ba bisa ka'ida ba, yana mai cewa mataki ne mai hadari na yaki da cutar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China