Wannan shiri tuni ya samu amincewar kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, da kuma majalisar gudanar da sha'anin mulki ta kasar Sin.
A karkashin wannan sabon tsarin, 'yan kasuwa su ne ke da alhakin aiwatar da harkokin rarraba mai a kasar, kuma gwamnati za ta dauki alhakin sa ido ne wajen kula da tabbatar da tsaron makamashi na kasa, da kuma tabbatar da ganin albarkatun suna biyan muradun jama'ar kasa baki daya.
A yanzu dai an bayyana wannan shiri da aka jima ana sa ran gabatar da shi wanda a halin yanzu mahukuntan kasar Sin suka yi amanna cewa sabon tsarin zai tabbatar da ingantuwar al'amurra a kasar ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Garambawul din yana kunshe ne cikin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13 na shekarar 2016 zuwa ta 2020.
Shirin yana kara tabbatar da aniyar mahukuntan kasar wajen zurfafa yin gyare gyare a kamfanonin mai da iskar gas mallakar gwamnatin kasar, kuma zai baiwa kamfanoni damar samun karuwar masu zuba jari a fannin albarkatun mai da iskaar gas. (Ahmad Fagam)