in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya fiye da 140 sun yi kira da a kara kokari tare domin kawar da kangin talauci da kiyaye hakkin dan Adam
2017-06-14 10:23:03 cri

Ranar 13 ga wata, a madadin kasashe fiye da 140 na duniya, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva Ma Zhaoxu, da wakilan sauran hukumomin kasa da kasa dake kasar Switzerland, sun fidda wata sanarwar hadin gwiwa mai taken "yin kokarin tare domin kawar da kangin talauci da ma kiyaye hakkin dan Adam", a yayin taron kwamitin harkokin hakkin dan Adam na MDD karo na 35 da ya gudana a birnin na Geneva, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kansu, wajen raya makomar dan Adam mai wadata kuma mai bunkasuwa tare, da kuma daukar matakan kiyaye hakkin dan Adam.

Kasashe fiye da 140 ne suka ba da wannan sanarwa ta hadin gwiwa, wadanda yawancinsu kasashe ne maso tasowa, da ma wasu kasashe masu sukuni. A madadin wadannan kasashe, mista Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, yanzu mutane fiye da miliyan dari 8 ne suke fama da talauci a duniyarmu. Kana kawar da talauci, wata muhimmiyar hanya ce ta kara azama, da kiyaye hakkin dan Adam. Mista Ma ya ce,

"Yadda za a sassauta da kawar da talauci yadda ya kamata, a kokarin kara samar da sharadi na kara azama da kiyaye hakkin dan Adam, kalubale ne da kasashen duniya suke fuskanta tare. Kuma kamata ya yi kasashen duniya su rubanya kokarinsu a wasu fannoni kamar haka."

A cikin wannan sanarwar, mista Ma ya yi bayani da cewa, da farko, a gaggauta raya kasa mai dorewa, a kuma girmama ikon ko wace kasa na zaben hanyarta ta yaki da kangin talauci, da raya kasa mai dorewa da kanta. Na biyu, a dauki mabambantan matakai tare, a kara bunkasa ababen more rayuwar jama'a a wurare masu fama da talauci, a samar wa matalauta hidimomin kiwon lafiya, tarbiya, da raya al'adu da dai sauransu, kana a kara samar da guraben aikin yi, a kokarin kyautata kwarewar kasashe na tsayawa da kafafunsu. Na uku kuma, a tsaya tsayin daka kan samun adalci a zamantakewar al'ummar kasa, a tabbatar da dukkan jama'a sun ci gajiyar bunkasuwar kasa da samun wadata tare. Na hudu, a inganta hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar yaki da talauci. Kamata ya yi a kiyaye da raya tattalin arzikin duniya da ke bude kofa ga kowa, a kafa sabuwar huldar kasa da kasa ta fuskar yaki da talauci, wanda zai mayar da hadin gwiwa da samun nasara tare a gaban komai, a kuma kara azama kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe maso tasowa da masu sukuni, da kuma tsakanin kasashe maso tasowa. Har ila yau, dole ne MDD ta taka muhimmiyar rawa wajen kara azama kan yaki da talauci a duniya.

A karshe, Mista Ma Zhaoxu ya yi bayani da cewa, da sauran riba a kaba, wajen tabbatar da manufar yaki da kangin talauci a duk duniya. Don haka kamata ya yi kasashen duniya su hada kansu, a kokarin cimma burin kau da kangin talauci daga duniyarmu cikin hanzari. Mista Ma ya ce,

"Ya dace mu yi kokari ba tare da kasala ba, wajen raya makomarmu ta dan Adam, wadda za ta kasance mai wadata, kuma wadda ke samun ci gaba mai dorewa tare!"

A lokacin da mista Ma Zhaoxu yake zantawa da manema labaru daga baya kuma, ya bayyana cewa, a madadin kasashe fiye da 140 na duniya, kasar Sin ta ba da wannan sanarwar hadin gwiwa, inda aka yi kira da a raya makomar dan Adam, maras kangin talauci, kuma ana samun ci gaba mai dorewa tare, a kokarin kara kaza azama, da kiyaye hakkin dan Adam, lamarin da ya dace da moriyar bai daya ta kasashen duniya, don haka sanarwar ta samu amincewar sassa daban daban. Mista Ma ya ce,

"Kawar da talauci, da kara azama, da kiyaye hakkin dan Adam, su ne burin bai daya na dukkanin kasashe masu tasowa, wanda kuma shi ne burin wasu kasashe maso sukuni. Wadanda suka ba da wannan sanarwar hadin gwiwa sun hada da kasar Girka. Wannan ya nuna cewa, matsayinmu dangane da kawar da talauci, da kara azama da kiyaye hakkin dan Adam ya samu amincewar kasa da kasa. "

Ban da haka kuma, mista Ma Zhaoxu ya ce, kasar Sin ta dauki shekaru da dama ta samun nasarar fitar da mutane miliyan dari 7 daga kangin talauci, hakan ya kasance muhimmiyar gudummowa ga sha'anin kare hakkin dan Adam a duniya. Kaza lika kasar Sin tana fatan bai wa sauran kasashe masu tasowa wasu kyawawan fasahohi nata, da matakan da ta dauka, dangane da kawar da talauci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China