Firaminista Li Keqiang na kasar Sin ya yi kira ga mahukuntan kasar da su dukufa wajen yiwa ayyukan gwamnati gyaran fuska ta hanyar mayar da hankali kan rage yadda ake ba da amincewa da tsarin tafiyar da harkokin mulki, mika harkokin tafiyar da mulki ga kananan ma'aikata da inganta hidimomi da yadda ake tafiyar da harkoki.
Mr Li wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ta kafar talabijin. Ya ce shirin yin kwaskwarima da kasar ke aiwatarwa wani juyin-juya hali ne ga gwamnati kanta. Ya ce muddin aka rage abubuwan dake kawo tarnaki ga harkokin tafiyar da mulki kana aka inganta hidimomi, hakika kasar za ta samu damar kirkiro yanayin kasuwa mai adalci da kara tabbaci ga kasuwannin mataki da zai baiwa jama'a damar yin kirkire-kirkire.
Ya kuma ce kamata ya yi kasar Sin ta ci gaba da rage yadda ake sanya hannu kan wasu ayyuka ta hanyar takaitawa gwamnati amfani da karfin iko.
Haka kuma kamata ya yi gwamnati ta rika saukaka matakan amincewa, karfafa san ido da inganta hidimomi.(Ibrahim)