Firaminista Li Keqiang na kasar Sin ya yi kira ga daukacin Sinawa dake zauna a kasashe daban-daban na duniya da su shiga a dama da su a shirin hadin gwiwar kasar da ragowa kasashen duniya game da harkokin kirkire-kirkire da tattalin arziki.
Li wanda ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da wakilai a taron majalisar Sinawa 'yan kasuwa da masu masana'antu dake ketare karo na biyu a nan birnin Beijing, ya ce tattalin arzikin kasar Sin yana bunkasa yadda ya kamata kuma gwamnati tana da tabbacin cimma nasarar manufofin bunkasuwa kamar yadda aka tsara a duk shekara.(Ibrahim Yaya)