Zaihid al-Khatoni, memban majalisar dokokin kasar Iraki mai kula da aikin tsugunar da fararen hula ya bayyana wa 'yan jarida cewa, bayan cin abinci, fararen hula kimanin 900 dake matsugunin U2 a Hasan Sham dake gabashin birnin Mosul sun kamu da cutar guban abinci.
Zaihid al-Khatoni ya kara da cewa, an kai fararen hular da suka hadu da wannan larura asibiti domin samun jiyya, kuma mafi yawansu mata ne da tsoffi da kuma yara. Kawo yanzu ana kulawa da su yadda ya kamata, ba a kuma samu rahoton rasa rayuka sakamakon matsalar ba.
Bisa alkaluman da hukumar ba da taimako ta kasar Iraki ta fitar, an ce, yakin kwace birnin Mosul da aka fara daga watan Oktoban bara, ya riga ya tilasawa fararen hula sama da dubu 700 kauracewa gidajensu. Ya zuwa yanzu kuma, ana ci gaba da dauki ba dadi a yammacin birnin na Mosul. (Fatima Liu)