Yawan mutanen da suka fita daga kangin talauci a shekarar 2016 a kasar Sin ya kai miliyan 12 da dubu 400
Ofishin dake kula da aikin taimakawa masu fama da kangin talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana a yau Talata cewa, adadin mutanen da suka fita daga matsi na talauci a shekarar bara a kasar Sin, ya kai mutum miliyan 12 da dubu 400, adadin da ya zarce burin da aka tsara, wato na rage yawan masu fama da talauci da mutum miliyan 10, wanda hakan ke nuna cewa, an bude sabon shafi ke nan tun a shekarar farko, ta kokarin kawar da talauci tsakanin al'ummar kasar.
Kakakin ofishin watsa labaru, na ofishin taimakawa masu fama da talauci Su Guoxia, ta bayyana cewa a shekarar bara, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, da hukumomin kudi na lardunan kasar, sun tanaji kudi da yawan su ya kai Yuan biliyan 100, don taimakawa masu fama da matsanancin talauci. A kuma bana, za a kara zuba jari a wannan fanni, da aiwatar da manufofin taimakawa matalauta, don tabbatar da cimma burin kara rage masu fama da fatara da adadin mutum miliyan 10. (Zainab)