in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An taimakawa talakawan Ningcheng ta hanyar raya sassan da suka dace da su
2017-03-01 20:15:14 cri

Mahukunta a kasar Sin sun raya garin Ningcheng dake kudancin birnin Chifeng a yankin Mongolia ta cikin gida ta hanyar samar da dabarun shuka tsirrai a cikin manyan rumfuna, da inganta kiwon dabobbi, da 'ya'yan itatuwa, matakin da ya zamo jigo na kawar da talauci a garin, ya kuma sanya mutane dake wurin jin dadin zaman rayuwa.

Sha'anin shuke-shuke a cikin manyan rumfuna na daya daga cikin manyan sassa uku a garin Ningcheng. Ya zuwa karshen shekarar 2016, yawan yankunan da aka shuke bisa wannan tsari ya kai muraba'in kilomita 260, an kuma samu kudi daga wannan fanni da yawan su ya kai Yuan biliyan 3.7.

A daya hannun kuma, yawan kudin da kowane manomi ya samu daga wannan fasaha ya karu da Yuan 4100, bisa makamancin lokaci na shekarar da ya gabata, wanda kuma hakan ke nuna an samu nasarar da aka cimma ta kawar da mutanen da yawansu ya kai dubu 11 daga kangin talauci.

A halin yanzu, mutanen dake garin Ningcheng sun fi son sha'anin shuke-shuke a manyan rumfuna, a matsayin sana'ar da ta fi samar da kudin shiga gare su, da ma kawar da talauci gaba daya. (Zainab)

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China