in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da dakaru wajen kashe fararen hula a Kongo Kinshasa
2016-08-16 10:59:21 cri
A jiya Litinin 15 ga wata, ta bakin kakakinsa, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya ba da sanarwar yin Allah wadai da wasu dakarun dake dauke da makamai game da harin da suka kai a wani kauyen dake gabashin kasar Kongo Kinshasa, inda suka kashe fararen hula da dama, tare da yin kira da a gurfanar da masu hannu a gaban kotu tun da wuri.

Sanarwar ta ce, an ba da labarin cewa, wasu dakaru da aka nuna tababa su mambobin kungiyar ADF (Allied Democratic Forces) mai adawa da gwamnatin Uganda suka kashe fararen hula sama da 10 a ranar 13 ga wata a wani kauyen dake jihar Nord-Kivu ta kasar Kongo Kinshasa. Ban Ki-moon ya girgiza kwarai kan wannan lamarin, tare da yin Allah wadai da harin da babbar murya. Haka kuma, ya jajanta wa iyalan wadanda suka mutu da gwamnatin Kongo Kinshasa.

Bugu da kari, sanarwar ta ce, daga watan Oktoba na shekarar 2014 zuwa yanzu, 'yan kungiyar ADF sun riga sun kashe fararen hula sama da dari daya a yankin dake gabashin kasar Kongo Kinshasa. Ban Ki-moon ya nanata cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD za su ba da taimako ga gwamnatin kasar wajen tinkarar barazanar da kungiyoyi masu dauke da makamai suke kawo wa bisa ka'idojin MDD.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China