in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A wani bangare na shawo kan matsalar yunwa, Burundi ta cire haraji kan wasu kayayyakin abinci da ake shigar da su kasar
2017-03-05 13:02:01 cri
Gwamnatin Burundi ta cire haraji kan wasu kayayyakin abinci da ake shigar da su kasar, biyo bayan matsananciyar yunwa da ta addabi yankuna da dama na kasar dake gabashin nahiyar Afrika.

Kakakin gwamnatin kasar, Philippe Nzobonariba ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da sakamakon taron majalisar zartaswar kasar na makon jiya.

A bara, gudumomi da dama na kasar sun fuskanci matsalar fari, al'amarin da ya yi mummunar tasiri ga yawan abincin da kasar ta sa ran samu.

A cewar Philippe Nzobonariba, nan ba da dadewa ba, za a sanar da jerin kayayyakin abincin da aka dage musu haraji. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China