in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Kasar Sin ya yi kira da a kara karfafa hadin kai wajen yaki da ta'addanci
2017-06-09 13:19:29 cri

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga al'ummomin kasashen waje, nakalci sabbin dabarun da kungiyoyin ta'addanci ke amfani da su, tare da kara inganta hadin kai don yakarsu.

Da ya ke jawabi a jiya, yayin taron kwamitin sulhu na MDD da ya mai da hankali kan barazanar da ayyukan ta'addanci ke wa tsaro da zaman lafiya a duniya, Wu Haitao ya ce a baya-bayan nan an kai hare-hare kasashen Masar da Afghanistan da Birtaniya da Faransa da Iran da sauran wurare, abun da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Ya ce ta'addanci babban abokin adawa ne ga bil adama, kuma mumunan tasirinsa ya wuce misali, ya na mai jadadda cewa, babu wata kasa da za ta iya magancewa ko kare kanta daga ta'addanci ita kadai.

Har ila yau, Wu Haitao ya yi kira da a dauki matakai da za su samu karbuwa ga dukkan kasashen duniya, wadanda za su magance ayyukan ta'addanci tun daga tushe da dakile yaduwar 'yan ta'adda da datse musu hanyoyin samun kudi da kuma yaki da manufofinsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China