Cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya domin ranar Ma'aikata ta duniya, shugaban kungiyar Francis Dzifa Ahadzi ya bayyana damuwa kan yadda kasar Ghana ta gaza amincewa da yarjejeniyoyin hukumar ILO.
Hukumar ta ILO ta yi kiyasin cewa, haddura da cututtuka da ake gamuwa da su a bakin aiki na sanadin mutuwar mutane miliyan 2.3 a kowace shekara.
Sanarwar ta ce, kungiyar na son amfani da ranar, wajen yin kira ga gwamnati a matsayin bukata ta gaggawa, da ta kafa dokar kare lafiyar ma'aikata, ta kuma kafa hukuma da za ta rika kula da batutuwan da suka shafi kare lafiyar ma'aikata a dukkan bangarori tare kuma da gaggauta amincewa da yarjejeniyoyin hukumar ILO dake da alaka da tabbatar da kariya da lafiyar ma'aikata a wuraren aiki.
Kungiyar ta kuma tunatarwa ma'aikatan Ghana cewa, tabbatar da kariya da lafiya a wuraren aiki hakki ne da ya rataya a wuyan kowa kuma hakki ne na bil'adama.
Ana bikin ranar ma'aikatan ne a duk shekara, domin yabawa irin gudunmuwar da ma'aikata ke baiwa wajen raya kasashensu. (Fa'iza Mustapha)