Jakadan Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta dauki wasu kwararan matakai domin dakilewa da kuma bada kariya daga gurbatar teku.
Lin Shanqing, mataimakin daraktan gudanarwa a hukumar kula da al'amurran teku na kasar Sin, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron MDD game sha'anin teku.
A dangane da batun kiyaye halittun cikin teku, kasar Sin tana daukar matakan inganta yankunan teku da dukkan yankunan da suka shafi koramu da teku domin kiyaye halittun dake rayuwar a cikinsu, inji Mista Lin.
A cewarsa, ta hanyar wadannan dokoki da matakai ne, gwamnati za ta iya bibiyar yanayin da yankunan tudu da na teku ke ciki, kuma za ta dauki dukkan matakan da suka dace a lokutan da suka dace.
Shirin kiyaye yankunan teku da muhallin halittun ruwa sun hada da albarkatun dake ruwa da da na gabar teku, kamar halittun dake rayuwa a cikin tekun, da tsirran dake kewaye da tekun wadanda suna da matukar muhimmanci wajen dawamar da ketu da koramu.(Ahmad Fagam)