in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane miliyan guda ne ke neman haramta amfani da roba sau daya
2017-06-07 14:03:19 cri
Za a gabatar da wani korafi, da mutane sama da miliyan 1 suka rattabawa hannu, wanda ke neman haramta amfani da roba sau daya a duniya nan da shekaru 5 masu zuwa, ga hukumar kare muhalli ta MDD, domin mara baya ga gangaminta na Clean Seas mai rajin tsaftace tekuna.

Wannan na zuwa ne, a daidai lokacin da wata sanarwar da hukumar kare muhallin ta MDD ta fitar ke cewa, kasashe sama da 20 sun nuna goyon bayansu ga gangamin na Clean Seas, wanda ke kira ga gwamnatoci da masana'antu da daidaikun mutane su kawo karshen amfani da kayayyakin roba sau daya da kuma daina sanya sinadaran roba cikin kayan kwalliya, wadanda su ne jigo wajen gurbata tekuna, kawo shekarar 2022. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China