in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da kasashen Afrika sun jaddada muhimmancin tabbatar da yunkurin samun dauwamammen ci gaba ya zuwa shekarar 2030
2016-09-24 13:01:11 cri

A jiya Jumma'a, kasar Sin da kasashen Afrika sun kira taro mai jigon "tabbatar da hakkin bil Adam a fannonin tattalin arziki da al'umma da al'adu ta hanyar tabbatar da yunkurin neman samun bunkasuwa mai dorewa ya zuwa shekarar 2030" a yayin da ake gudanar da taron hukumar hakkin bil Adam ta MDD karo na 33 a birnin Geneva. Zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin MDD dake birnin Geneva Ma Zhaoxu ya ba da jawabi, inda ya bayyana muhimmancin tabbatar da wannan yunkuri domin kiyaye hakkin bil Adam a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma da kuma al'adu tare da matsayin da kasar Sin ta dauka kan wannan batu, kana ya gabatar da matakai da Sin ta dauka da kuma sakamakon da ta samu a kan wannan aiki.

Zaunannen wakilin kungiyar AU dake birnin Geneva Jean-Marie Ehouzou da zaunannen wakilin kasar Afrika ta Kudu dake birnin Mxakato-Diseko da kuma wakilan zaunanniyar tawagar kasar Portugal dake birnin da ofishin babban kwamishinan kula da harkokin hakkin bil Adam na MDD da kwamitin hakkin bil Adam a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma da kuma al'adu na MDD da kuma kungiyar 'yan kwadago ta kasa da kasa sun halarci taron tare da ba da jawabai.

Jakada Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, neman samun bunkasuwa na da muhimmanci sosai wajen kare hakkin bil Adam musamman ma a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma da kuma al'adu. Ya ce, har kullum kasar Sin tana dora muhimmanci kan neman samun bunkasuwa, kana ta tabbatar da muradun karni na MDD cikin sauri. A halin yanzu, Sin ta samu nasara a fannoni da dama wajen tabbatar da burin neman samun bunkasuwa mai dorewa ya zuwa shekarar 2030.

Mista Ma ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen Afrika a dukkan fannoni cikin sahihanci, domin cimma burin neman samun bunkasuwa mai dorewa ya zuwa shekarar 2030 tare, kana za ta yi kokarin taimaka wa kasashen Afirka samun ci gaba bisa ci gaban da ita kanta ta samu, ta yadda za a samu moriyar juna, domin amfana wa jama'ar Sin da na kasashen Afrika gaba daya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China