Kakakin hukumar kididdiga ta kasar Sin Xing Zhihong, ya furta a yau Litinin cewa, cikin watan Afrilu da ya gabata, tattalin arzikin kasar Sin na cikin wani yanayi mai kyau. Ana kuma samun karuwa a fannonin samar da kayayyaki, da bukatu a kasuwannin kasar, da samun karin guraben ayyukan yi. Sa'an nan farashin kayayyakin kasar na karuwa sannu a hankali, yayin da ake kokarin zurfafa gyare-gyare kan tsarin aikin samar da kayayyaki, da sabunta sana'o'in da ke ciyar da tattalin arzikin kasar gaba.
Duk a cikin watan na Afrilu, kudin masana'antun kasar Sin ya karu da kashi 6.5% idan an kwatanta da na makamancin lokaci a bara. (Bello Wang)