Da yake tabbatar da hakan a jiya Talata, babban jami'in hukumar ta NDRC Wang Dong, ya ce bikin na wannan rana, zai bada damar tallata tamburan da kamfanoni daban daban ke da su, da irin gwagwarmaya da masu sana'o'i ke sha, da ma irin nasarorin da suke samu a fannin cinikayya.
Majalissar kolin kasar Sin ce dai ta amince da sanya ranar 10 ga watan Mayu na ko wace shekara, a matsayin ranar bikin tambarin kasar Sin, wadda a bana aka gudanar da irin ta ta farko a yau Laraba. (Saminu Hassan)