Hukumar kula da harkokin inshora ta kasar Sin CIRC, ta ce ribar ta kai Yuan trillion 1.59 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 230 daga watan Junairu zuwa Maris.
Ya zuwa karshen watan Maris, hukumar ta samu ribar da ya kai Yuan Trillion 16.2, wanda ya daga da kashi 7 cikin dari daga farkon shekarar nan.
Hukumar ta alakanta ci gaban da aka samu da yadda aka shiryawa tunkarar kalubale da gudanar da aiki yadda ya kamata.
Tun daga farkon shekarar nan ne, jami'an dake kula da harkokin kudi ke aiki don kare aukuwar asara a matsayin wata muhimmiyar hanya ta samun riba.
A watan da ya gabata ne, hukumar CIRC ta sanar da shirya wani gangami yaki da take ka'idoji domin farfado da yanayin kasuwa, da daukar matakan yaki da zuba jari na karya, da rashin gudanar da harkoki yadda ya kamata tare da bayar da bayanan bugi. (Fa'iza Mustapha)