A jimilce mutane 90 ne aka tabbatar da mutuwarsu, a yayin da ake ganin adadin zai wuce haka a nan gaba, in ji mista Sharma.
Koda yake ba a tabbatar da dalilin da ya hadasa wannan fashewa ba nan take, amma wasu majiyoyi sun bayyana cewa hadarin ya abku ne dalilin wasu sandunan Gelatine, wani sinadari mai hadarin gaske da ake amfani da shi wajen hakar ma'adinai, da aka ajiye su tare da butallan gas a wani gidan da ke makwataka da wurin da hadarin ya faru. (Maman Ada)