in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari ga 'yan sanda a kasar Indiya
2017-04-25 11:18:16 cri
Rahotanni daga 'yan sandan kasar Indiya na cewa, a jiya Litinin, dakaru masu adawa na Naxalite dake kasar Indiya, sun kai hari kan 'yan sanda a Chattisgarh dake tsakiyar kasar, wanda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 24, tare da raunata wasu mutane 6.

An dai kai harin ne kan wasu rukunin sojojin share-fage na 'yan sandan kwamitin tsakiya na kasar da misalin karfe 1 na rana. An kuma yi musayar wuta har ta tsawon wasu awoyi a tsakanin bangarorin biyu. An ce, dakarun Naxalite kimanin 300 ne suka kai harin, kawo yanzu ba a san yawan mutanen da suka mutu ko suka raunata a sakamakon harin ba.

Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Indiya suka bayar, an ce, kasar ta riga ta kara tura 'yan sanda zuwa yankin da harin ya auku, don farautar dakarun na Naxalite da suka tsere.

Bayan faruwar harin, firaministan kasar Indiya Narendra Modi, ya bayyana a kan shafin twitter sa cewa, ya yi Allah wadai da harin.

An kafa kungiyar dakarun Naxalite a shekaru 60 na karnin da ya gabata, kuma yawan mambobin ta ya kai kimanin mutum dubu 10, wadanda su kan gudanar da ayyuka a yankuna masu talauci dake gabas da tsakiyar kasar Indiya, suna kuma kai hari ga sassan gwamnatocin kasar, don haka gwamnatin kasar ta dauke su a matsayin babbar barazana da ake fuskanta a kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China