Wani babban jami'in hukumar jiragen kasa ta kasar Indiya ya bayyana cewa, yayin da hadarin ya faru, lokacin daddare ne, fasinjoji da dama suna barci, don haka yawan mutane da suka mutu ko raunata ya yi yawa. Yanzu hukumar ta tura ma'aikata da dama wurin domin bada ceto. An riga an gano gawawwaki 91 a wurin, kana an kai mutanen da suka ji raunuka masu tsanani zuwa asibiti.
Firaministan kasar Indiya Narendra Modi ya bayyana ta shafin Twitter cewa, ya nuna jajantawa ga iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin, da kalubalanci hukumomin da abin ya shafa da su yi bincike nan da nan. (Zainab)