in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana ta jaddada kudurinta na karfafa kungiyar ECOWAS
2017-05-31 09:23:59 cri
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya jaddada kudurinsa na karfafa Kungiyar ECOWAS mai raya tattalin arzikin kasashen Africa ta yamma, yana mai cewa yanzu ne ya kamata kasashen yankin su hada kansu.

Ya ce ana sa ran kasuwar yammacin Afrika mai mutane miliyan 350 zai fadada zuwa mutane miliyan 500 nan da shekaru 20, yana mai cewa abun nufi shi ne, samun muhimmiyar kasuwar yankin wadda za ta yi la'akari da bukatun kasashen yankin, domin samar da dimbin damammaki ga al'umma, idan aka yi aiki tukuru da kirkiro sabbin manufofi da dabaru da kuma cinikayya.

Akufo-Addo ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin bikin cika shekaru 42 da kafuwar kungiyar ECOWAS, wadda cibiyar tabbatar da hadin kan yakin ta shirya.

Ya ce kamata ya yi samar da ingantacciyar kasuwa ta bai daya a yankin ECOWAS ya zama babbar manufar al'ummar kasar Ghana da sauran jama'a da gwamnatocin yammacin Afrika.

Ya ce fara la'akari da yammacin Afrika da nahiyar baki daya kafin daidaikun kasashe, nuna kishin kasa ne, saboda haka abun da zai inganta yammacin Afrika, zai inganta tare da ciyar da daidaikun kasashe gaba. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China