in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta jadadda kudurinta na hada kai da kasashen yankin ECOWAS
2017-04-29 12:52:06 cri
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya jaddada kudurin kasarsa, na ingata hadin kai tsakanin kasashen da suke yanki daya.

Nana Akufo Addo na wannan jawabi ne a jiya, lokacin da yake ganawa da Salou Djibo, shugaban kwamitin hadin gwiwa na aiwatar da shirin 'yancin cinikayya na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS.

Shugaba Akufo-Addo ya ce tun bayan kafuwar kungiyar ECOWAS shekaru 42 da suka gabata da kuma yarjejeniyar 'yancin cinikayya da ke akwai kusan shekaru 40, har yanzu, yankin yammacin Afrika bai cimma gajiyar cinikayya tsakanin kasashen ba, saboda rashin kyakkyawan kudurin shugabanci na karfafa ayyukan kungiyar.

Ya kara da cewa, da yadda adadin al'ummar yankin ke iya kai wa miliyan 500 kawo shekarar 2035, yankin na da dimbin damarmakin kasuwanci da cinikayya da zuba jari da kuma kaifin basira.

Kididdiga ta nuna cewa, cinikayya tsakanin kasashen yankin bisa alkaluman GDP a shekarar 2013 ya kai kashi 9 cikin dari, adadin da ya yi kadan, idan aka kwatanta da sauran yankunan duniya.

Shirin na 'yancin cinikayya shi ne muihimmiyar hanyar da Kungiyar ECOWAS take amfani da ita wajen inganta cinikayya cikin 'yanci a yankin yammacin Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China