in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Burundi za ta kauracewa tattaunawa kan sasanta rikicin kasar na 2015 da za a yi a Tanzania
2017-02-16 10:53:46 cri

Wata sanarwa da Gwamnatin Burundi ta fitar jiya da daddare, ta ce Gwamnatin ta yanke shawarar kauracewa tattaunawa domin sasanta rikicin da ya auku a kasar cikin shekarar 2015, da za a yi a Arusha na kasar Tanzani, daga yau Alhamis 16 zuwa 18 ga wata.

Sanarwar da kakakin Gwamnatin kasar Philippe Nzobonariba ya fitar, ta ce Gwamnatin ba za ta tura wakilai zauren tattaunawar ba. Tana mai cewa, al'ummar kasar na bukatar goyon bayan kasashen waje, amma kuma,suna da damar da za a mutunta zabinsu game da tsarin tattaunawar.

Kakakin gwamnatin ya ce gayyatar mahalarta tattaunawar da za a yi karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Tanzania,kuma mai shiga tsakani a batun tattaunawar Benjamin Mkapa, na kunshe da kurakurai, inda ya ce an shigar da karar wasu daga cikin wadanda aka gayyata a gaban kotun Burundi, bisa hannu da suke da shi wajen yi wa tsaron kasar tarnaki.( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China